Yadda Buratai ya samu kyakkyawar tarbo bayan sallar juma’a a Kaduna (Hotuna)

- Babban Hafsan Sojojin Najeriya ya yi sallar juma’a a masallacin Sultan Bello da ke Kaduna a jiya juma’a - Daruwan al’ummar musulmi a masallaci sun yi masa kyakkyawar tarbo
- Al’ummar musulmi sun yi farin cikin saduwa da shi a masallaci Babban Hafsan Sojojin Najeriya (COAS), Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya samu kyakkyawar tarbo daga al’ummar musulmi bayan sallar juma’a a masallacin Sultan Bello da ke Kaduna babban birnin jihar a ranar juma’a, 28 ga watan Yuli. Daruwan al’ummar musulmi sun yi murnar saduwa da babban hafsan sojojin yayin da suka yaba da kuma girmama masa a lokacin da yake kokarin shiga motarsa. Babban hafsan sojin ya sanya tufafin kaftan mai ruwan kasa zuwa sallar juma’a a lokacin da hotuna ke nuna shi yana murmushi da daruruwan masoyansa wadanda ke masa fatar alheri. Idan dai baku manta ba a makon da ta gabata NAIJ.com ta kawo muku cewa babban hafsan sojojin Najeriya ya ba Ibrahim Attahiru, babban kwamandan Operation Lafiya Dole da ke jihar Borno wa’adi na kwanaki 40 ya kama Abubakar Shekau shugaban kungiyar ‘yan ta’adda Boko Haram.





No comments

Powered by Blogger.