Menene dalilin da yasa aka kashe Ahmadu Bello Sardauna?

A yau an kwashe sama da shekaru 52 da suka gabata kenan da bindige gamji dan kwarai, Firimiya na farko kuma daya tilo na yankin Arewacin Najeriya, Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato. 




Sir Ahmadu Bello ya kwanta dama ne a ranar Juma’a, 15 ga watan Janairu cikin watan Azumi na shekarar 1966, shekau shidda da samun yanci, inda wasu kananan hafsoshin soji suka far masa a daren juma’an suka yi masa ruwan harsasai. Manjo Chukwuemeka Kaduna Nzeogwu, wanda ya jagoranci kai harin ya bayyana dalilansa na kashe Sardauna; da suka hada da girman kai, cin hanci da rashawa, son kai, da kokarin kaddamar da jihadi a Najeriya. Sai dai an tabbatar gaba daya wadannan dalilan daya dogara akansu duk shaci fadi ne, don kuwa ko bayan da aka kashe Sardauna, an tarar da Banki na binsa bashi ne ma, maganan son kai kuwa, ai a wancan lokaci kowane yankin kasar nan kokari take ta gina jama’anta da yankinta. Wani na hannun daman Sardauna, Sheikh Abubakar Gumi ne da kansa ya fada ma Manjo Nzeogwu karya yake yi game da zargin Sardauna da yake na kokarin kaddamar da jihadi, inda Shehin Malamin ya fada masa Sardauna bai taba tara makamai a ko ina ba don shirin yaki. Manya cikin wadanda aka hallaka a wannan rana, a cikin mutane 22, sun hada da Firai ministan Najeriya, Abubakar Tafawa Balewa, Firai ministan yankin yammacin kasar nan Samuel Akintola, janar Zakari Mai Malari, Ademulegun, Ahmad Ben Musa, Yakubu Pam, Largema, Kur Muhammad. Ga jerin sunayen mutanen da aka hallaka nan: Ahmadu Bello Sardauna Abubakar Tafawa Balewa

Samuel Ladoke Akintola
Festus Okotie-Eboh ministan kudi Shugaban hafsan Soji Birgediya Samuel Ademulegun da matarsa Latifat Ademulegun
Ahmed Ben Musa Maigadin Sardauna Hafsatu Bello Uwargidar Sardauna Zarumi, shima ma’aikaci a gidan Sardauna Ahmed Pategi Direban Sardauna Kanal Ralph Shodeinde Birgediya Zakariya Maimalari
Kanal Kur Mohammed
Sauran sun hada da: Laftanar kanar Arthur Unegbe Sajan Daramola Oyegoke abikin aikin Nzeogwu, daga baya Nzeogwun da kansa ya kashe shi Yohana Garkawa Kofur Musa Nimzo Akpan Anduka Hagai Lai Philip lewande Idan mai karatu ya duba jerin mutanen nan, zai fahimci dukkanin mutanen da aka kashe abokanan Sardauna ne a siyasance ko a addininance, ko kuma yanki daya ya hada su. Yanzu karanta jerin mutanen da suka shirya tare da zartar da kashe wadannan bayin Allah da na ambata a sama: Manjo Kaduna Nzeogwu Manjo Adewale Ademoyega Manjo Emmanuel Ifeajuna Manjo Timothy Onwuatuegwu Manjo Chris Anuforo Manjo Humphrey Chukwuka Manjo Don Okafor Kyaftin Ogbo Oji Sai mu kara tambayar kawunan mu, wai menene dalilin kashe Ahmadu Sardauna da Abubakar Tafawa Balewa?

No comments

Powered by Blogger.